Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiPortugal na sa ran Cristiano Ronaldo zai koma tawagar ƙasar a watan...

Portugal na sa ran Cristiano Ronaldo zai koma tawagar ƙasar a watan Nuwamba

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal, Pedro Proença, ya bayyana cewa ana sa ran Cristiano Ronaldo zai koma tawagar ƙasar a watan Nuwamba bayan an cimma matsaya tsakanin hukumar, koci Jorge Jesus da ’yan wasan tawagar.

Proença ya ce hukumar da kocin da kuma ’yan wasan duk suna son Ronaldo ya dawo, kuma shi ma ɗan wasan a shirye yake ya koma tawagar.

Ya ƙara da cewa abokan wasansa na son ganin ya dawo, yana mai bayyana Ronaldo a matsayin gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na kowane lokaci.

Wannan na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce kan Ronaldo da kuma batun barinsa sansanin tawagar Portugal.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments