Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC-PCC ya buƙaci ’yan Najeriya da suka cancanci yin zaɓe su fito su karɓi katunan zaɓensu na PVC, tare da tabbatar musu cewa ƙuri’unsu za su yi tasiri a babban zaɓen 2027.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara aikin raba katunan zaɓen a faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya fitar ranar Juma’a, ADC-PCC ya yi watsi da ikirarin cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta yi maguɗin sakamakon zaɓe domin samun nasara, tana mai bayyana irin waɗannan kalamai a matsayin yaɗa bayanan da ba su dace ba da nufin hana jama’a fita yin zaɓe.
Ologbondiyan ya ce:
“Ku je ku karɓi katin zaɓenku. Katin zaɓenku shi ne ƙarfin ku, kuma shi ne tabbacin cewa za ku yi zaɓe a ranar 16 ga Janairu, 2027.”
Ya yi zargin cewa wasu masu goyon bayan APC ne ke yaɗa tsoron maguɗin zaɓe domin su hana ’yan Najeriya shiga harkokin zaɓe, saboda fargabar cewa jama’a za su ƙi jam’iyyar sakamakon yadda take tafiyar da mulki.
Ya ce:
“APC ta san ba za ta iya cin zaɓe na gaskiya, adalci da sahihanci ba bayan jefa ’yan Najeriya cikin yunwa, wahala da rashin tsaro. Shi ya sa take son ’yan Najeriya su yarda cewa za a rubuta sakamakon zaɓe. Ƙarya ce. Zamanin rubuta sakamakon zaɓe a ɗakunan otal ya wuce har abada.”
Ologbondiyan ya bayyana cewa matakan kariya da ake da su a tsarin zaɓe, ciki har da Dokar Zaɓe da aka yi wa kwaskwarima, na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS da kuma shafin INEC na duba sakamakon zaɓe na IReV, za su taimaka wajen hana maguɗi.
Ya kuma yi nuni da yadda wayewar kan ’yan Najeriya kan harkokin siyasa ke ƙaruwa, yana mai cewa jama’a sun ƙara azama wajen amfani da ƙuri’unsu domin sauya makomar ƙasar.
Ya ƙara da cewa: “Za a kare kowace rumfar zaɓe. Za a ƙirga kowace ƙuri’a, kuma kowace ƙuri’a za ta yi tasiri. ’Yan Najeriya sun fi kowane lokaci azama wajen kwato ƙasarsu ta hanyar zaɓe.”
ADC-PCC ya buƙaci sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin mata da ƙungiyoyin fararen hula da su wayar da kan waɗanda suka cancanci yin zaɓe domin su karɓi katunansu tare da amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya.
Kwamitin ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ADC, ƙarƙashin ɗan takararta na shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, zai tura wakilan jam’iyya zuwa dukkan rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar domin sa ido kan tsarin zaɓe, kare ƙuri’u da kuma hana duk wani yunƙuri na satar nasarar da jama’a suka zaɓa.