Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaBabban burin tafiyar TMG shi ne kawar da gwamnatin Tinubu - Barista...

Babban burin tafiyar TMG shi ne kawar da gwamnatin Tinubu – Barista Dantani

Lauyan ya ce an dauko tafiyar Tinubu Must Go ne saboda bukatar yan Najeriya na kawar da gwamnatin APC da ta gaza a bangarori daban-daban

Lauya mai zaman kansa, Nuhu Dantani, ya bayyana cewa babban abin da yake gabansu a yanzu shi ne kokarin ganin an kawo karshen gwamnatin APC karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Dantani ya bayyana hakan ne a wata hira da wakiliyar ICONIC TIMES, Aisha Ibrahim, kan shirin da suka fara na Tinubu Must Go (TMG) gabanin babban zaben 2027.

Dantani da takwaransa na Kano, Barista Abba Hikima, ne ke jagorantar tafiyar, wadda suka ce an assasa ta ne saboda halin matsin tattalin arziki da sauran matsalolin da suke ganin ’yan Najeriya ke fuskanta.

A makon da ya gabata, Abba Hikima ya sanar da cewa ya janye daga goyon bayan tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, bayan wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a a kafafen sada zumunta da ta nuna cewa tikitin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi ya samu rinjaye.

Sai dai Dantani ya ce ba ya cikin masu goyon bayan Obi ko Kwankwaso.

“Ni ban taba yin Peter Obi ba kuma ban taba nuna cewa ina yin Peter Obi ba ko ina mara baya ga Peter Obi ba. Don saboda dan uwana Abba Hikima ya mara Peter Obi bai zama ni na goy bayan Peter Obi ba.”

Ya kara da cewa kowa na da ’yancin yin zabi bisa akidarsa, yana mai cewa tafiyar TMG ta samo asali ne daga korafe-korafen jama’a kan yadda suke kallon gwamnatin Tinubu.

“Kowa da matsayarsa kuma kowa da akidarsa kuma kowa da yancinsa. Duk da akwai tafiya da muka bullo na Tinubu Must Go. Wannan tafiya da muka bullo bisa ra’ayin kanmu ne da kuma yadda ’yan Najeriya suke koke, suka nuna damuwa da rashin jin dadin shugabancin Bola Tinubu.”

Dantani ya ce ba shi da wata alaka da tafiyar Obi/Kwankwaso, yana mai bayyana cewa ba zai goyi bayan abin da ya kira akidar Biyafara ba.

A cewar lauyan:

“Amma ni ban da alaka da tafiyar ko mara wa Obi/Kwankwaso baya. Ban taba yi ba kuma ban yi ba kuma ba zan yi ba. Saboda ba yadda zan yi na yadda da masu ra’ayin Biyafara su mulke mu saboda ba wai ban yadda da ingancin Peter Obi ba ne, amma akidarsu na Biyafara din nan da suke kokarin kawo shi yasa na ke tsoro.”

Ya ce ba shi da matsala da Kwankwaso, yana mai yabawa irin rawar da ya ce tsohon gwamnan Kano ya taka wajen talakawa a lokacin mulkinsa.

Lauyan ya ce:

“Ban da matsala da Kwankwaso. Shugaba ne, jagora ne wanda kowa ya san abubuwan da ya yi ga talakawa na Arewacin Najeriya musamman na jihar Kano lokacin da yake gwamna. Ban da matsala da shi ba wai saboda shi dan Arewa ba ne, a’a, shi ma wancan ba don saboda Ibo ba ne amma akidarsu ta Biyafara kwata-kwata ba ta min ba.”

Lauyan ya kuma zargi gwamnatin tarayya da cire tallafin man fetur, wanda ya ce ya kara tsananta matsin tattalin arziki, tare da kasa shawo kan matsalar tsaro.

Ya ce:

“Duk da mun san cewa ba shi ya kawo matsalar tsaro ba, duk da shi ma gada ya yi, amma ya yi alkawarin zai magance kuma ba a magance ba kuma kara tsananta yake. Kuma kayan masarufi ya yi tsada, gidajen haya ya yi tsada, komai ya tashi.”

Dantani ya ce tafiyar TMG ba ta da wata manufa ta kudi ko wata boyayyar manufa, yana mai cewa idan APC ta yi tayin ba su wani abu, za su iya shiga jam’iyyar.

A kalamansa:

“Ba wata manufa da muke da shi, musamman ma ni da kika ganni Hamza Nuhu Dantani ba wanda zai ce miki ni na karbo wannan tafiya, to nawa za a ba ni? Ni ma mai bayarwa ne ba don ina nuna alfahari ba, amma ni ma mai bayarwa ne,” cewar Dantani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments