Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKungiyar Musulmi ta soki Gwamnatin tarayya kan rashin ambaton Falasdinu a UNGA

Kungiyar Musulmi ta soki Gwamnatin tarayya kan rashin ambaton Falasdinu a UNGA

Ƙungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) Nigeria ta soki gwamnatin tarayya kan rashin ambaton Falasdinu a jawabin Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 (UNGA).

Ƙungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) Nigeria ta soki gwamnatin tarayya kan rashin ambaton Falasdinu a jawabin Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 (UNGA).

MPAC ta ce jawabin Najeriya mai sakin layi 24 ya mayar da hankali kan gyaran Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, sauyin yanayi, fasahar AI, bashin ƙasashe da yaƙi da ta’addanci, amma bai ambaci Falasdinu ko mafita ta ƙasashe biyu ba.

Ƙungiyar ta ce hakan ya bambanta da jawabin Najeriya a UNGA na 80, inda ta yi Allah-wadai da tashin hankalin da ake yi wa fararen hula a Gaza tare da sake jaddada goyon bayanta ga mafita ta ƙasashe biyu.

MPAC ta danganta sauyin da abin da ta bayyana a matsayin ƙara ƙarfafa dangantakar tsaro da diflomasiyya tsakanin Najeriya da Isra’ila, ciki har da yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen biyu suka rattaba hannu a watan Agustan 2025.

Ƙungiyar ta buƙaci Najeriya ta shiga ƙarar Afirka ta Kudu kan Isra’ila a Kotun Ƙasa da Ƙasa (ICJ), tare da yin kira ga gwamnati ta fito fili kan matsayinta game da Falasdinu, tana mai cewa idan matsayar Najeriya ta sauya, ya kamata ’yan ƙasar su san dalilin hakan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments