Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanci‘Yan sanda sun kama mutum shida kan zargin karkatar da kaya na...

‘Yan sanda sun kama mutum shida kan zargin karkatar da kaya na N20bn

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kama wasu mutane shida da ake zargi da kasancewa mambobin wata ƙungiyar masu karkatar da kayan da aka shigo da su cikin ƙasar, waɗanda ake zargin sun karkatar da kaya da darajarsu ta haura Naira biliyan 20 cikin kimanin shekaru 19.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kama wasu mutane shida da ake zargi da kasancewa mambobin wata ƙungiyar masu karkatar da kayan da aka shigo da su cikin ƙasar, waɗanda ake zargin sun karkatar da kaya da darajarsu ta haura Naira biliyan 20 cikin kimanin shekaru 19.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Jamiu Lateef da Abubakar Amadu, waɗanda ’yan sanda suka bayyana a matsayin shugabannin ƙungiyar.

An ce mutanen biyu na da tireloli da dama da suke amfani da su wajen jigilar kayayyaki, tare da wasu kadarori da zuba jari a Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin.

An kama su ne bayan masu shigo da kaya sun kai ƙorafi kan bacewar kayayyakin da suka shigo da su ta tashar jiragen ruwa ta Apapa.

’Yan sandan sun ce ƙungiyar na amfani da dabarar samun kwangilar jigilar kayayyaki daga tashar jiragen ruwa zuwa wasu jihohi, musamman arewa da gabashin Najeriya, kafin su karkatar da kayan zuwa wasu wurare su sayar.

Wata majiya ta ’yan sanda ta ce yawancin mambobin ƙungiyar an taɓa kama su a baya, amma bayan an sake su daga gidan yari suna komawa aikata laifin.

A wani sabon lamarin, ana zargin ƙungiyar da karkatar da forklifts, yadudduka da faranti da aka shigo da su, waɗanda darajarsu ta kai kusan Naira biliyan uku.

Rahotanni sun ce waɗanda ake zargin sun karɓi aikin jigilar kayan daga Legas zuwa Kano, amma maimakon su kai kayan Kano, sai suka karkatar da su zuwa Ojota, inda suka sauke su tare da sayar da su ga waɗanda ke karɓar kayan.

Jamiu Lateef ya amsa wa ’yan sanda cewa sun ɗauki kayan ne daga tashar jiragen ruwa, amma suka karkatar da su zuwa Ojota inda suka sayar da su.

Shi ma Abubakar Amadu, mai shekaru 45, ya ce ya fara wannan harkar tare da Jamiu kimanin shekaru 19 da suka gabata bayan sun haɗu a lokacin da suke aikin tuƙin manyan motoci.

’Yan sandan sun ce yayin binciken lamarin, sun gano wasu daga cikin yaduddukan da aka karkatar a wata kasuwa da ke Agege, inda mai kayan ya gane su.

Binciken ya kuma kai ga kama wasu da ake zargin su ne masu karɓar kayan, direbobin motocin da ake amfani da su da kuma shugabannin ƙungiyar biyu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Legas, SP Abimbola Adebisi, ta bayyana kamen a matsayin babbar nasara da sashen ya samu.

Ta ce bincike na ci gaba da gano sauran mambobin ƙungiyar tare da kwato wasu daga cikin kayayyakin da ake zargin ƙungiyar ta karkatar a ayyukanta na baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments