Ƙungiyar Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gaggauta ɗaukar matakan gaggawa tare da ayyana dokar ta-baci a gidan yarin Kurmawa da ke Kano, bisa zargin barkewar cutar kwalara.
Ƙungiyar ta ce aƙalla fursunoni shida ne suka mutu cikin mako guda, yayin da wasu ke ci gaba da karɓar magani sakamakon abin da ake zargin barkewar cutar.
Amnesty ta yi gargadin cewa rashin ɗaukar matakin gaggawa na iya jefa ƙarin rayukan fursunoni cikin haɗari.
A cikin wani saƙo da ta wallafa a Facebook, Amnesty ta buƙaci a garzaya da fursunonin da ke cikin mawuyacin hali zuwa asibitoci domin samun kulawar lafiya da ta dace.
Ta kuma ce akwai yiwuwar adadin waɗanda suka mutu ya fi wanda aka bayyana, yayin da ake zargin cutar na ci gaba da yaɗuwa a tsakanin fursunonin.
Ƙungiyar ta bayyana damuwarta musamman kan waɗanda ke tsare yayin da suke jiran shari’a, tana mai cewa yanayin cunkoso da rashin tsafta a wasu gidajen yari na iya ƙara haɗarin yaɗuwar cututtuka.
Amnesty ta kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta inganta yanayin tsare fursunoni, ta hanyar samar da isasshen abinci, tsafta da kulawar lafiya, tare da magance matsalar mutanen da ke shafe dogon lokaci a gidan yari ba tare da kammala shari’arsu ba.
Ƙungiyar ta ce ɗaukar matakan gaggawa domin dakile barkewar cutar da kuma kare lafiyar fursunoni na da muhimmanci wajen tabbatar da mutunta haƙƙin ɗan Adam da ƙa’idojin kula da waɗanda ke tsare a gidajen yari.