Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta ce za ta mayar da martani bayan hare-haren sama da Pakistan ta kai a wasu sassan Afghanistan, inda ta ce an kashe fararen hula akalla huɗu.
Rahotanni sun ce hare-haren na ranar Alhamis sun shafi lardunan Kandahar, Paktia da Khost.
Pakistan ta bayyana cewa ta kai hare-haren ne kan wurare 10 da take zargin ana amfani da su wajen adana da kuma harba jiragen sama marasa matuka da ake kai hare-hare da su cikin Pakistan.
Ministan Yaɗa Labarai na Pakistan, Attaullah Tarar, ya ce hare-haren an shirya su ne kan wuraren da aka gano suna da alaƙa da hare-haren jiragen sama marasa matuka da aka yi ƙoƙarin kai wa Pakistan.
Sai dai gwamnatin Taliban ta musanta cewa ita ce ta harba jiragen marasa matukan da Pakistan ke magana a kai.
Mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce hare-haren sun janyo asarar rayukan fararen hula tare da yin barazanar cewa Afghanistan za ta ɗauki matakin da ya dace.
Ƙarin arangamar na zuwa ne yayin da dangantakar Pakistan da Afghanistan ke ƙara tabarbarewa sakamakon zarge-zargen kai hare-haren ƙetare iyaka.
Ƙasashen China, Turkiyya, Qatar da Saudi Arabiya na cikin waɗanda ke ƙoƙarin shiga tsakani domin rage rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu, amma sabon tashin hankalin na iya ƙara dagula waɗannan ƙoƙarin.