Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeHarin bindiga ya jikkata mutum 11 a lardin Manisa da ke Turkiyya

Harin bindiga ya jikkata mutum 11 a lardin Manisa da ke Turkiyya

Akalla mutum 11 sun jikkata bayan wani mutum ya buɗe musu wuta a kusa da wata makarantar sakandare a lardin Manisa da ke yammacin Turkiyya.

Akalla mutum 11 sun jikkata bayan wani mutum ya buɗe musu wuta a kusa da wata makarantar sakandare a lardin Manisa da ke yammacin Turkiyya.

Bayan harbin, wanda ake zargin ya tsere daga wurin dauke da bindiga, daga bisani jami’an tsaro suka cafke shi. Rahotanni sun ce biyu daga cikin waɗanda suka jikkata suna cikin mawuyacin hali.

Hotunan bidiyon da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna wani mutum dauke da bindiga yana kusa da makarantar, kafin ya gudu daga wurin.

Har yanzu hukumomi ba su bayyana dalilin harin ba. Wasu kafafen yaɗa labaran Turkiyya sun ce wanda ake zargin ɗalibi ne mai shekaru 15, amma ba a tabbatar da wannan bayanin ba.

Ma’aikatar Ilimi ta Turkiyya ta ce lamarin ya jefa al’umma cikin alhini, tare da tura jami’ai zuwa Manisa domin gudanar da bincike.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments