Akalla mutum biyar sun mutu, yayin da wasu kuma suka ɓace bayan wata ƙaƙƙarfar guguwa ta afkawa yankunan gabashin Japan.
Guguwar ta haddasa ruwan sama mai ƙarfi a yankunan da ke kusa da Tokyo, lamarin da ya jefa dubban gidaje cikin duhu bayan katsewar wutar lantarki.
Jami’an kula da yanayi sun gargadi jama’a da su ci gaba da taka-tsantsan tare da kasancewa cikin shiri saboda barazanar ci gaba da samun mummunan yanayi.
Guguwar ta kuma tilasta dakatar da wani babban baje kolin wasannin bidiyo a Tokyo, yayin da aka soke ɗaruruwan jirage tare da dakatar da wasu ayyukan jiragen ƙasa.