Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDangote zai zuba sama da Dala biliyan 10 wajen samar da wutar...

Dangote zai zuba sama da Dala biliyan 10 wajen samar da wutar lantarki a Afirka

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana shirin zuba sama da dala biliyan 10 a fannin samar da wutar lantarki cikin shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa, domin taimakawa wajen magance matsalar makamashi da kuma bunƙasa masana’antu a Najeriya da sauran sassan Afirka.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Al Jazeera, inda ya ce rashin isasshiyar wutar lantarki da kuma rashin tabbas kan wasu manufofin gwamnati na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga zuba jari da ci gaban masana’antu a nahiyar Afirka.

Ya ce ana duba yiwuwar karkatar da wasu jarin kamfanonin Dangote, ciki har da harkar ƙarafa, zuwa fannin samar da wutar lantarki.

Ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen da kamfanin ke yi domin ganin an samu gagarumin sauyi a fannin makamashi a Afirka.

Dangote ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda sama da mutum miliyan 600 a Afirka ke rayuwa ba tare da samun isasshiyar wutar lantarki ba, yana mai cewa nahiyar na bukatar magance matsalar cikin gaggawa.

A cewarsa, wutar lantarki na da muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziki, masana’antu da samar da ayyukan yi, yana mai jaddada cewa ba za a samu cikakken ci gaba ba tare da ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments