Kungiyar Eyes on the Environment Initiative (EEI), tare da hadin gwiwar Nature News, SusLab, Green Foundation, Eco Media Central da Youth Green Hub, ta bukaci gwamnatin Jihar Kano ta karfafa manufofin rage yawan sharar robobi.
Kungiyoyin sun yi wannan kiran ne yayin wani aikin tsaftace muhalli da suka gudanar a gidan adana namun daji na Audu Bako da ke Kano ranar Lahadi, 20 ga Satumba, domin bikin Ranar Tsaftace Duniya ta 2026.
An gudanar da aikin ne karkashin taken, “Strive for 5!!! From Clean Plates to Clean Streets!!!”, inda mutane 42 suka shiga, ciki har da mata 14 da matasa biyu.
Masu aikin sun kwashe awa daya da mintuna 50 suna tsaftace wasu sassan lambun dabbobin, inda suka tattara kimanin buhunan shara 15.
Mafi yawan sharar da aka tattara sun hada da kwalaben roba, ledojin ruwan sachet, tsumman roba, cokulan roba, sandunan lollipop, kwantenan abinci, kofunan roba da sauran robobin da ake amfani da su sau daya sannan a jefar.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta rabawa Iconic Times, ta yaba wa dukkan masu aikin sa kai da suka ba da lokacinsu da karfinsu domin ganin an gudanar da aikin.
“Mun gode wa dukkan masu aikin sa kai da suka ba da lokacinsu, karfinsu da jajircewarsu domin ganin an gudanar da wannan aikin tsaftace muhalli. Zuwan su na nuna cewa kare muhalli ba aikin gwamnati da kungiyoyi kadai ba ne, nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa,” in ji kungiyar.
Kungiyar ta ce yawan robobin da aka tattara ya sake nuna bukatar daukar kwararan matakai domin magance matsalar gurbatar muhalli tun daga tushe.
Ta bukaci gwamnatin Kano ta karfafa manufofin rage sharar gida, sake amfani da kayayyaki, sarrafa shara da kuma bunkasa tsarin tattalin arzikin da ke rage almubazzaranci.
Kungiyar ta kuma bukaci a samar da tsarin ERP wanda zai sanya kamfanonin da ke kera, shigo da, rarrabawa ko sayar da kayayyakin roba su dauki karin nauyi kan illar kayayyakinsu ga muhalli.
Ta ce ya kamata masu kera kayayyaki, masu shigo da su, masu kamfanoni, dillalai da masu sayar da kayayyaki su samu takamaiman nauyin da ya rataya a wuyansu wajen tattarawa da sarrafa robobin da suka shiga kasuwa bayan an yi amfani da su.
Kungiyar ta kuma ba da shawarar daukar matakan rage amfani da ledojin sayayya, ciki har da sanya karin kudi kan ledojin roba da ake amfani da su sau daya tare da karfafa amfani da jakunkunan da za a iya sake amfani da su.
Ta ce ya kamata a gudanar da duk wani kudin da aka samu daga irin wannan tsari cikin gaskiya, tare da karkatar da shi zuwa ayyukan sake sarrafa shara, tattara robobi, shirye-shiryen tsaftace muhalli da wayar da kan jama’a.
Kungiyar ta ce aikin tsaftace muhalli yana da muhimmanci, amma bai kamata ya maye gurbin ingantaccen tsarin sarrafa shara ba.