Wasu ‘yan bindiga sun kashe tare da fille kan MaiGarin Lafagu da ke ƙaramar hukumar Bagudo a jihar Kebbi.Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, inda ya ce an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a kisan.
Ya ce har yanzu ba za a bayyana sunan Mai Gari da aka kashe ba, yana mai cewa rundunar za ta fitar da ƙarin bayani bayan kammala bincike.
SP Bashir ya ce, “Eh, gaskiya ne an kashe shugaban ƙauyen Lafagu da ke ƙaramar hukumar Bagudo. Mun kama wasu mutane dangane da lamarin, kuma za mu bayar da cikakken bayani daga baya.”