Wata mummunar fashewar gas a wani gida a Sokoto ta yi sanadin mutuwar Farfesa Hassan Muhammad Maishanu na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ’yarsa, Husnah, mai shekaru 21.
Lamarin ya faru ne a ranar 9 ga Satumba, 2026, yayin da Husnah, wadda daliba ce a matakin farko na karatun Software Engineering, ke girkin abinci. Mahaifinta ya shiga kicin domin duba matsalar gas, kafin daga bisani aka ji wata babbar fashewa.
Mahaifiyar Husnah, Zaliha Aliyu Gidan Kanawa, ta ce mijinta ya fito daga kicin cikin mummunan yanayi sakamakon konewa, yayin da aka samu Husnah da kanin ta, Sudais, suma cikin mawuyacin hali.
An kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, inda Husnah ta rasu a daren ranar. Mahaifinta kuma ya ci gaba da jinya a sashen kula da marasa lafiya masu tsanani (ICU), kafin daga bisani ya rasu.
Dalibai da abokan aikinsa sun bayyana marigayi Farfesa Maishanu a matsayin malami mai saukin kai, jajircewa da taimakon dalibai. Sun ce ya kasance mai ladabi kuma yana kulawa da wadanda ke bukatar taimakonsa.
An haifi Farfesan a Sokoto a shekarar 1970, kuma ya samu digirin digirgir na PhD a fannin Botany daga jami’ar Usmanu Danfodiyo. Ya zama farfesa a watan Nuwamba 2025, kuma ya rasu ya bar mata da ’ya’ya 13.