Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn harbi masu zanga-zanga a Neja kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37

An harbi masu zanga-zanga a Neja kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37

Jami’an tsaro a Minna, Jihar Neja, sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare da harbin bindiga yayin zanga-zangar da aka gudanar kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu a hannun Hukumar NSCDC.

Jami’an tsaro a Minna, Jihar Neja, sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare da harbin bindiga yayin zanga-zangar da aka gudanar kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu a hannun Hukumar NSCDC.

Daruruwan mutane ne suka fito zanga-zangar a rana ta biyu, inda wasu suka kai hari kan gine-ginen gwamnati. Gwamna Umar Bago ya sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 domin dakile rikicin.

An kama mutanen ne a samamen aka kai wuraren haƙar ma’adinai a yankin Wushishi-Lukoto bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba. Har yanzu ba a tabbatar da ainihin dalilin mutuwarsu ba, duk da zargin cewa cunkoso da rashin isasshen iska a wurin tsarewar na iya kasancewa cikin abubuwan da suka haddasa mutuwar.

Wani da ya tsira, Dauda Shehu, ya ce an cunkushe mutane da yawa a ɗaki guda ba tare da isasshen iska ba, lamarin da ya sa suka fara fama da wahalar numfashi.

A halin yanzu, an dakatar da kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, yayin da gwamnatin tarayya ta ce za a gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa mutuwar mutanen.

SourceAljazeera
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments