A cewar Daraktar ayyukan jin ƙai ta WFP, Ross Smith yayin jawabinta gaban zaman Majalisar da ya gudana a birnin Geneva, ta ce yunwa za ta kara tsananta, ganin yadda a yanzu haka al’ummar yankin ke cikin mawuyacin hali saboda ƙawanyar watanni 18 da mayaƙan RSF suka yi wa zagayen Al-Fashir.
Babbar jami’ar WFP ta ce daga watan Janairu za a rage tallafin kayan abincin da ta ke shigarwa zuwa kashi 70 a yankunan da ke fama da yunwa, yayin da za a ga raguwar kashi 50 a cikin 100 a yankunan da iyakar riciki ne ya taɓasu ba tare da tsanantar yunwa ba.
Tun bayan tsanantar rikicin Sudan da ya faro a watan Afrilun 2023, wanda ya juye zuwa yaƙi mafi muni da ƙasar ta gani a tarihi, masana suka fara hasashen fuskantar matsananciyar yunwa, sai dai WFP ta ce matsalar ta ta’azzara ne bayan janye tallafin da ke shigowa don taimakawa wajen samar da abinci ga ɗimbin mutanen da ke rayuwa a sansanonin wucin gadi.
Yakin ya raba miliyoyin mutane ya raba da muhallansu inda da dama ke rayuwa a ƙasashen maƙwabta.
Daraktar ayyukan ta WFP Ross Smith, ta bayyana cewa matuƙar ba a samu kuɗin tafiyar da ayyukan agajin ba, zuwa watan Aprilun baɗi, hukumar ba ta da tallaffin da za ta iya miƙawa mabuƙata a Sudan.