Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiFitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Olu Jacobs, ya rasu

Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Olu Jacobs, ya rasu

Fitaccen jarumin Nollywood ya rasu a yau, 16 ga Satumba, 2026, bayan ya shafe shekaru yana taka rawar gani a fina-finai.

Fitaccen jarumi a masana’antar fina-finai ta Najeriya, Ou Jacobs ya rasu.

Ɗansa, Olusoji Jacobs, ne ya sanar da rasuwar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba.

Ya ce:

“Cikin godiya ga Allah bisa rayuwar da ta yi mai ma’ana da da kuma kalubale daban-daban, muna sanar da rasuwar mijinmu, uba, kakana da kawunmu ƙaunatacce.”

“Oludotun Baiyewun Jacobs (MFR). 11/07/1942 – 16/09/2026. Muna kira ga dukkan masu rubutu a yanar gizo da masu tasiri a kafafen sada zumunta da su mutunta sirrin iyalinmu a wannan lokaci.”

Olu Jacobs ya fara sana’ar wasan kwaikwayo ne ta hanyar fitowa a wasu shirye-shiryen talabijin na Birtaniya da fina-finai na ƙasa da ƙasa.

Ya halarci makarantar Holy Trinity, inda ya kasance mamba a ƙungiyoyin muhawara da wasan kwaikwayo na makarantar.

Jacobs ya samu ƙwarin gwiwar shiga harkar wasan kwaikwayo ne bayan da ya halarci ɗaya daga cikin bukukuwan wasan kwaikwayo na shekara-shekara na marigayi Cif Hubert Ogunde a Colonial Hotel da ke Kano.

Bayan haka, ya samu takardar izinin shiga Birtaniya, inda ya tafi domin karantar wasan kwaikwayo.

A Birtaniya, Jacobs ya yi karatun wasan kwaikwayo a The Royal Academy of Dramatic Arts da ke London.

Ɗ

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments