Rundunar tsaron sararin samaniyar Saudiyya ta ce ta kakkabo wani jirgi mara matuki da ake zargin kungiyar Houthi da harbawa zuwa yankin birnin Makka mai tsarki.
A cewar Manjo Janar Turki Al-Malki, kakakin rundunar kawancen da ke yaki da Houthi a Yemen, an gano jirgin mara matukin ne a kudancin Makka da misalin karfe 6:50 na yammacin Talata, 15 ga Satumba, kafin ya shiga yankin da aka haramta zirga-zirgar jiragen sama.
Al-Malki ya ce rundunar tsaron ta dauki matakin gaggawa tare da lalata jirgin, yana mai cewa za a ci gaba da daukar matakan kare Masallatan Harami biyu da kuma fararen hula da mazauna kasar.