Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce safarar man fetur ta ɓarauniyar hanya zuwa ƙasashen maƙwabta na daga cikin manyan dalilan da ke haifar da tsadar man fetur a Najeriya.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan matsalolin da ke tattare da kasuwar man fetur da kuma bambancin farashinsa tsakanin Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.
A cewarsa, farashin man fetur a wasu ƙasashen maƙwabta ya fi na Najeriya da kashi 30 zuwa 50 cikin ɗari.
Ya ce wannan babban bambancin farashin na ƙara bai wa masu fatauci da masu safarar man fetur ba bisa ƙa’ida kwarin gwiwar fitar da man daga Najeriya zuwa ƙasashen waje domin samun riba.
Hamshakin attajirin ya bayyana cewa ci gaba da fitar da man fetur ta haramtacciyar hanya na iya ƙara matsin lamba kan wadatar man a cikin gida, wanda hakan ke iya yin tasiri kan farashinsa.
Dangote ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan da za su rage safarar man fetur ba bisa ƙa’ida ba tare da tabbatar da isasshen man fetur a kasuwar cikin gida.