Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciA yau matatar Dangote za ta fara siyar da hannun jarinta kan...

A yau matatar Dangote za ta fara siyar da hannun jarinta kan Naira 525

Matatar Dangote ta fara sayar da sababbin hannun jarinta ga jama’a, a wani mataki da kamfanin ya bayyana a matsayin babbar dama ga masu zuba jari da kuma ci gaban kasuwar hannayen jari ta Najeriya.

Sayar da hannun jarin ta fara ne a ranar Litinin, 14 ga Satumba 2026, inda kamfanin ya sanya farashin kowane kaso a kan N525.

A cewar sanarwar kamfanin, an fitar da sababbin hannun jari guda biliyan 4.1, kuma ana sa ran sayar da su zai samar da kusan Naira tiriliyan 2.15.

Kamfanin ya ce mafi ƙarancin adadin hannun jarin da mutum zai iya saya guda 10 ne, wanda darajarsu ta kai N5,250. Za a ci gaba da karɓar buƙatun sayen hannun jarin har zuwa ranar 13 ga Oktoba 2026, bisa sharuɗɗan da aka bayyana a takardun sayar da hannun jarin.

Wannan dai shi ne karon farko da aka bai wa jama’a damar mallakar wani kaso kai tsaye a Matatar Dangote, wadda ake bayyana a matsayin matatar mai mafi girma a Afirka.

Kamfanin ya ce kuɗaɗen da za a samu daga sayar da hannun jarin za su taimaka wajen faɗaɗa ayyukan matatar, gudanar da wasu muhimman tsare-tsaren zuba jari da kuma ƙara darajar hannun jarin masu saka jari.

An kuma buɗe damar sayen hannun jarin ga ƙananan masu zuba jari, manyan masu zuba jari da sauran waɗanda suka cancanta a Afirka.

Kamfanin ya bayyana matakin a matsayin wata muhimmiyar dama ga masu zuba jari su kasance cikin mallakar ɗaya daga cikin manyan kamfanonin masana’antu da makamashi a nahiyar Afirka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments