Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya yi kira ga matasan Arewa da su ƙara ƙaimi wajen yaɗa manufofi da nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da goyon bayan sake zaɓensa a shekarar 2027.
Akpabio ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, ciki har da cire tallafin man fetur da gyaran tsarin canjin kuɗi, sun taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Akpabio ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake karɓar wata babbar tawaga daga ƙungiyar Northern Ethnic Groups Assembly a Abuja.
Ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ta aiwatar sun fara haifar da wasu alamun ci gaba, musamman wajen ƙara kuɗaɗen shiga da kuma inganta amincewar masu zuba jari a ƙasar.
Akpabio ya buƙaci matasan Arewa da su taka rawar gani wajen bayyana wa jama’a manufofin gwamnatin Tinubu da abin da ta cimma, domin samun ƙarin goyon baya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.