Wasu mata a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna sun fara yin tsarin iyali saboda tsananin fargabar sace-sace da garkuwa da mutane da ke addabar yankunansu, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.
A ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026, an ruwaito sace mutane biyar a Mararaban Kajuru da ke mazabar Kufana a Ƙaramar Hukumar Kajuru.
Baya ga firgici da radadin da al’umma ke fuskanta sakamakon sace mutane daga gidajensu, wasu mata sun bayyana damuwa kan abin da ka iya faruwa da su idan suka faɗa hannun masu garkuwa da mutane.
Daga cikin abubuwan da matan ke fargaba da su akwai cin zarafi ta hanyar amfani da ƙarfi, samun ciki ba tare da so ba, da kuma yiwuwar komawa gida su fuskanci kyama ko rashin karɓuwa daga al’umma.
Rahoton ya nuna cewa matsalar rashin tsaro ta shafi al’ummomi da dama a Kajuru, ciki har da Ungwan Barde, Ungwan Galadima, Maro Bauda, Kampany da Dantaro da ke mazabar Maro.
Sauran yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da Janwuriya a mazabar Buda, Kallah da Gefe a mazabar Kallah, Kuturah a mazabar Kufana, da Mokoro Waziri a mazabar Idon, da sauran yankuna.
Matsalar sace-sace da garkuwa da mutane na ci gaba da jefa al’ummar yankunan cikin fargaba, yayin da mata musamman ke bayyana damuwa kan yadda rashin tsaron ke shafar rayuwarsu da makomarsu.