Jam’iyyar APM ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin ƙwarewa wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar Najeriya.
Jam’iyyar ta ce gwamnatin tarayya na ƙin amincewa da ainihin halin da ƙasar ke ciki, musamman saboda ikirarin da take yi cewa harkokin tsaro sun inganta a faɗin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, APM ta kuma yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na rage girman matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a ƙasar.
Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da matsalar rashin tsaro a duniya a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu, tana mai kira ga gwamnati da ta ɗauki ƙarin matakai masu inganci domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.