Wasu ‘yan daba sun far wa tawagar ‘yan jarida da suka je ɗaukar rahoto a taron ƙaddamar da shugabannin ƙungiyoyin magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala taron, inda ‘yan dabar suka tare motar gidan rediyon Pyramid da tawagar ‘yan jaridar ke ciki, tare da farfasa gilasan motar da adduna da wuƙaƙe.
Daga cikin ‘yan jaridar da lamarin ya shafa akwai Abdulbaki Ali Ahmad Sharifai na Radio Guarantee da Yakubu Gwagwarwa na Pyramid Radio.