Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa na kujerar Sanatan Kano ta Arewa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, gabanin zaɓen 2027.
Sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar ta bayyana cewa Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, Manajan Daraktan Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, ne aka naɗa shugaban kwamitin.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr Ali Haruna Makoda, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin, yayin da tsohon Surveyor General na Tarayya, Surveyor Nadu Yahaya, zai zama sakatare.
Haka kuma, an naɗa tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Farouk Lawan, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin na farko, yayin da Saidu Garba Getso da Badamasi Ayuba za su kasance mataimakan shugaban kwamitin na biyu da na uku.
Tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Alhaji Yusuf Tumfafi, ne aka naɗa Darakta-Janar na kwamitin, tare da wasu mataimakan daraktoci.
Kwamitin ya ƙunshi wakilai daga ƙananan hukumomi 13 na Kano ta Arewa, waɗanda suka haɗa da Shanono, Bagwai, Gwarzo, Kabo, Rimin Gado, Tofa, Dawakin Tofa, Bichi, Ghari, Tsanyawa, Dambatta, Makoda da Gabasawa.
Sanata Barau ya umarci mambobin kwamitin da su kai saƙon jam’iyyar APC ga al’umma a sassa daban-daban na Kano ta Arewa, tare da ƙara wayar da kan jama’a domin neman goyon baya ga ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Ya kuma bayyana cewa ayyukan gwamnatin APC sun bayyana a fili, inda ya buƙaci kwamitin da ya bayyana wa jama’a nasarorin da gwamnatin ta samu tare da neman gagarumin goyon baya a zaɓe mai zuwa.