Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu matasa a Najeriya na sayar da kodarsu domin samun kuɗin da za su gudanar da rayuwarsu.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, Atiku ya ce ya samu rahotannin da ya bayyana a matsayin masu tayar da hankali kan yadda matsin rayuwa ke tilasta wasu matasa shiga irin wannan hali.
Ya ce maimakon matasa su sayar da sassan jikinsu, ya kamata su kasance suna amfani da dabarunsu, tunaninsu da ƙirƙire-ƙirƙirensu wajen samun abin dogaro da kai.
Atiku ya kuma yi zargin cewa wasu matasa na sayar da kodarsu kan kuɗi har Naira miliyan 1.7.
Ya ce lamarin na buƙatar kulawa, musamman wajen samar da hanyoyin da za su taimaka wa matasa samun damar yin rayuwa cikin mutunci ba tare da shiga haɗarin lafiyarsu ba.