Ɗan wasan baya na Real Madrid, Antonio Rüdiger, ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasar Jamus ƙwallo.
Rüdiger mai shekaru 33 ya bayyana hakan ne a ranar Talata, bayan ya shafe shekaru yana wakiltar Jamus a wasannin ƙasa da ƙasa.
Ya ce ya yanke shawarar ne bayan dogon nazari, yana mai cewa lokaci ya yi da za a ba matasan ‘yan wasa damar samun gurbi.
Rüdiger ya kasance ɗaya daga cikin muhimman ‘yan wasan bayan Jamus a shekarun baya, inda ya wakilci ƙasar a manyan gasa da dama.
Duk da ritayar tasa daga tawagar ƙasa, Rüdiger zai ci gaba da buga ƙwallo a matakin kulob tare da Real Madrid.