Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAntonio Rüdiger ya yi ritaya daga buga wa Jamus ƙwallo

Antonio Rüdiger ya yi ritaya daga buga wa Jamus ƙwallo

Ɗan wasan baya na Real Madrid, Antonio Rüdiger, ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasar Jamus ƙwallo.

Ɗan wasan baya na Real Madrid, Antonio Rüdiger, ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasar Jamus ƙwallo.

Rüdiger mai shekaru 33 ya bayyana hakan ne a ranar Talata, bayan ya shafe shekaru yana wakiltar Jamus a wasannin ƙasa da ƙasa.

Ya ce ya yanke shawarar ne bayan dogon nazari, yana mai cewa lokaci ya yi da za a ba matasan ‘yan wasa damar samun gurbi.

Rüdiger ya kasance ɗaya daga cikin muhimman ‘yan wasan bayan Jamus a shekarun baya, inda ya wakilci ƙasar a manyan gasa da dama.

Duk da ritayar tasa daga tawagar ƙasa, Rüdiger zai ci gaba da buga ƙwallo a matakin kulob tare da Real Madrid.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments