.
Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, Tony Okocha, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya miƙa katin ga Fubara a jiya juma’a.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Fubara ya ce ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne da nufin bunƙasa haɗin kai da ci gaban jihar Ribas.
Fubara ya ce samun daidaito da jam’iyya mai mulki a matakin tarayya ya zama wajibi don tabbatar da zaman lafiyar siyasa da kuma ci gaba a faɗin jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa a yanzu da jihar Ribas ta haɗe a ƙarƙashin inuwa ɗaya da gwamnatin tarayya, aikin da ke gabansa na ƙarfafa jam’iyyar APC.
Bikin ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo (SAN).