Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da ƙara tsaurara matakan tsaro gabanin bikin Takutaha na 2026, wanda za a gudanar a ranar Talata, 1 ga Satumba.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundunar ta shirya tsare-tsare na musamman domin tabbatar da cewa bikin ya gudana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Bakori ya yabawa al’ummar Kano bisa yadda suka kasance suna gudanar da bikin cikin lumana tare da bin doka a shekarun baya. Ya kuma gode wa sarakunan gargajiya, malamai, shugabannin al’umma, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan haɗin gwiwar da suke bai wa rundunar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, an ce matakan tsaron sun haɗa da sintiri na sa’o’i 24, tattara bayanan sirri, binciken ababen hawa da mutane, da tura jami’an tsaro na musamman zuwa wuraren da ake sa ran za a gudanar da bikin.
Haka kuma, rundunar za ta mayar da hankali kan hanyoyin shiga da fita da kuma wuraren da ake ganin za su iya zama barazana ga tsaro.
Kwamishinan ya gargadi ’yan daba da masu neman tayar da hankali da su nisanci wuraren bikin, yana mai cewa rundunar ba za ta amince da duk wani tashin hankali, daba ko abin da zai kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba.
Ya ce duk wanda aka kama yana karya doka zai fuskanci gurfanarwa a gaban kotu domin ɗaukar matakin da doka ta tanada.
Rundunar ta kuma yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ƙungiyoyin sa-kai, sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da tsaro a jihar.
A ƙarshe, ’yan sanda sun buƙaci al’umma da su gudanar da bikin cikin lumana, su guji duk wani abu da zai iya haddasa rikici, tare da kai rahoton duk wani mutum ko abin da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko layukan gaggawa na rundunar.
Rundunar ta ce tana fatan bikin Takutaha na bana zai gudana cikin zaman lafiya, farin ciki da annashuwa.