Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Abba ta haramta kungiyar Hisbah da Ganduje zai kafa a Kano

Gwamnatin Abba ta haramta kungiyar Hisbah da Ganduje zai kafa a Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya haramta kafawa da gudanar da ƙungiyar Hisbah Fisabilillahi da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ke ƙoƙarin samarwa a ƙarƙashin gidauniyarsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan cikin wani umarni a ranar Juma’a, kamar yadda Kwamashinan Yaɗa Labarai Ibrahim Abdullahi Waiya ya shaida wa manema labarai.

Gwamnatin Kano dai ta ce yunƙurin kafa ƙungiyar “daidai yake da kafa wata hukumar tsaro da ka iya kawo wa zaman lafiyar al’umma barazana”.

Da yake isar da saƙon gwamnan, Waiya ya jaddada cewa hukumar Hisbah da dokar majalisar dokokin Kano ta kafa ce kaɗai hukumar da ke da izinin gudanar da ayyukan da suka shafi Shari’ar Musulunci a jihar.

“Saɓa wa doka ne ga duk wani mutum ko ƙungiya ko rukunin wasu mutane su taru, su tattaro, horar da, ko aika wani mutum da zummar aiwatar da wani aikin Hisbah ko wata ƙungiya mai kama da haka a jihar,” a cewar umarnin.

“Saboda haka, daga yau duk wasu ayyukan Hisbah Fisabilillahi haramtattu ne,” a cewar Kwamashina Waiya.

“Gwamna ya bai wa ‘yan sanda umarnin daga yanzu duk wanda aka gani da kakin wannan ƙungiya a kama shi.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments