Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bada umarnin janye sojoji daga wuraren binciken ababen hawa da ke titunan sassan ƙasar, domin komawa yaƙi da ƴan ta’adda, inda ya ce ƴan sanda za su maye gurbin su wajen samar da tsaro a kan hanyoyin.
Tun bayan rantsar da Janar Musa, wanda tsohon babban hafson Sojin ƙasar ne, ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa za a ga sauyi a fannin tsaro a cikin ƙanƙanin lokaci, yana mai alkawarin sake gina haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soji da sauran hukumomin tsaron ƙasar domin haɗa ƙarfi don yaƙar matsalar tsaron da ta addabi ƙasar mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika.
A cewar Janar Musa, Sojojin za su koma dazuka don tunƙarar ƴan ta’adda gaba da gaba da nufin murƙushe barazanarsu, yayin da jami’an ƴan sanda kuma za su mayar da hankali wajen tsaron cikin gida.