Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu sauƙin lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 idan aka kwatanta da zaɓen 2023.
Wike ya danganta hakan da rauni da rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa, yana mai cewa yawan sauya sheƙa da rashin haɗin kai sun rage musu ƙarfin kalubalantar Tinubu.
Ya ce adawa mai ƙarfi tana buƙatar tsawon lokaci wajen gina tsari da haɗin kai, maimakon sauya jam’iyya akai-akai domin neman damar tsayawa takara.
Wike ya kuma bayyana cewa ayyukan gwamnatin Tinubu cikin shekaru uku da suka gabata, musamman an Abuja, ba za a iya rage muhimmancinsu ba.