Manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa da shugabannin jam’iyyun siyasa sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Ƙasa, domin tabbatar da gudanar da kamfen ɗin zaɓen 2027 cikin lumana.
An gudanar da taron ne a Abuja ranar Talata ƙarƙashin jagorancin National Peace Committee (NPC), tare da haɗin gwiwar The Kukah Centre, gabanin fara kamfen ɗin zaɓen 2027 a ranar Laraba, 19 ga Agusta.
Sai dai Shugaba Bola Tinubu na APC da ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, ba su halarci taron ba. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ne ya wakilci Tinubu.
Daga cikin ‘yan takarar da suka halarci taron akwai Peter Obi na NDC, Adewole Adebayo na SDP da Omoyele Sowore na AAC.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya buƙaci ‘yan siyasa su mayar da hankali kan manufofi da hanyoyin magance matsalolin ƙasar, maimakon kai hare-haren kashin kai, kalaman ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.
Ya ce “zaɓe ba yaƙi ba ne,” illa gasa ce tsakanin ‘yan takara domin neman amincewar masu zaɓe.
Peter Obi ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su hukunta duk wani ɗan takara ko jam’iyyar da ta karya yarjejeniyar, ta hanyar ƙin zaɓen su.
Kwamitin Zaman Lafiya ya ce yarjejeniyar ba wata takarda ce ta al’ada kawai ba, domin tana da tushe a Kundin Tsarin Mulki, Dokar Zaɓe da kuma ƙa’idojin INEC.
Haka kuma, ‘yan sanda sun gargadi jam’iyyu da magoya bayansu da su guji amfani da ‘yan daba, makamai, barazana da kalaman tunzura jama’a yayin kamfen.