Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙara a kan Hukumar ICPC, inda yake neman diyyar Naira biliyan 10 bisa zargin hana iyalansa ganinsa yayin da yake tsare a hannun hukumar.
El-Rufai ya shigar da ƙarar ne ta hannun lauyansa, Ubong Akpan, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Ya kuma haɗa Shugaban ICPC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a cikin waɗanda ake ƙara.
A cikin ƙarar, tsohon gwamnan ya zargi ICPC da hana matarsa, Aishatu Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, damar ganinsa da kai masa abinci, magunguna da sauran abubuwan da yake buƙata.
Ya kuma zargi jami’an hukumar da tsarewa da kuma tsoratar da matarsa da ɗansa a ranar 7 ga Yuli.
El-Rufai na neman kotu ta tabbatar da cewa haƙƙoƙinsa na kundin tsarin mulki na ci gaba da aiki duk da kasancewarsa a tsare, tare da umartar ICPC da ta ba shi damar ganawa da iyalansa da lauyoyinsa cikin sauƙi.