Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiEl-Rufai ya bukaci ICPC ta biya shi diyyar biliyan 10 kan hana...

El-Rufai ya bukaci ICPC ta biya shi diyyar biliyan 10 kan hana iyalansa ganinsa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙara a kan Hukumar ICPC, inda yake neman diyyar Naira biliyan 10 bisa zargin hana iyalansa ganinsa yayin da yake tsare a hannun hukumar.

El-Rufai ya shigar da ƙarar ne ta hannun lauyansa, Ubong Akpan, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Ya kuma haɗa Shugaban ICPC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a cikin waɗanda ake ƙara.

A cikin ƙarar, tsohon gwamnan ya zargi ICPC da hana matarsa, Aishatu Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, damar ganinsa da kai masa abinci, magunguna da sauran abubuwan da yake buƙata.

Ya kuma zargi jami’an hukumar da tsarewa da kuma tsoratar da matarsa da ɗansa a ranar 7 ga Yuli.

El-Rufai na neman kotu ta tabbatar da cewa haƙƙoƙinsa na kundin tsarin mulki na ci gaba da aiki duk da kasancewarsa a tsare, tare da umartar ICPC da ta ba shi damar ganawa da iyalansa da lauyoyinsa cikin sauƙi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments