Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiJihar Zamfara ta horas da malamai 250 kan fasahar AI da dabarun...

Jihar Zamfara ta horas da malamai 250 kan fasahar AI da dabarun koyarwa na zamani

Gwamnatin Jihar Zamfara ta fara horas da malamai, masu tantancewa da jami’an gudanar da harkokin ilimi 250, domin inganta koyarwa da sakamakon karatu a jihar.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta fara horas da malamai, masu tantancewa da jami’an gudanar da harkokin ilimi 250, domin inganta koyarwa da sakamakon karatu a jihar.

Ana gudanar da horon ne ƙarƙashin shirin Global Standard Teacher Transformation Programme (GSTTP) na kwanaki 18, wanda aka fara a Zamfara College of Arts and Science (ZACAS) da ke Gusau.

A rana ta uku ta horon, mahalarta sun koyi amfani da fasahar ilimi da Artificial Intelligence (AI), sabbin hanyoyin koyarwa da koyo, yadda ake tsara CV da kuma dabarun sauyi da ci gaban ilimi.

An raba mahalartan zuwa rukuni-rukuni domin ba su damar samun cikakkiyar fahimta da kuma yin aikace-aikace kan darussan da ake koyarwa.

Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta jihar ta ce shirin na da nufin bai wa malamai dabarun zamani da sabbin hanyoyin koyarwa da za su dace da bukatun ilimin zamani.

Ma’aikatar ta ce amfani da fasahar zamani da AI wajen horar da malamai zai taimaka musu wajen fahimtar sauye-sauyen da ke faruwa da kuma inganta koyarwa a ajujuwa.

Ta ƙara da cewa ƙarfafa ƙwarewar malamai da masu gudanar da makarantu na da matuƙar muhimmanci wajen inganta shugabanci da sakamakon karatun ɗalibai.

Ana sa ran shirin GSTTP na kwanaki 18 zai bai wa mahalarta sabbin dabarun koyarwa da sauran hanyoyin zamani da za su taimaka wajen inganta harkar ilimi a Zamfara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments