Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya zargi wasu ‘yan siyasar Najeriya da hana ci gaban ƙasar da gangan.
Yayin jawabi a Legas a bikin cikar shekaru 15 na ‘Enough is Enough (EiE) Nigeria’, Sarki Sanusi ya ce wasu daga cikin ‘yan siyasa na kallon mukamin gwamnati a matsayin harkar taimakon kansu ko ta iyalansu, maimakon amanar rike al’umma.
Ya ce irin wannan hali shi ne babban dalilin da yasa Najeriya ba ta ci gaba yadda ya kamata ba.
A cewarsa, shugabanni kan yi watsi da damar da za su iya inganta ƙasar saboda suna mai da hankali kan muradun kansu.
“An yi wa kasar nan illa sosai, lokaci ya yi da ya kamata a tsagaita,” in ji shi.
Sarki Sanusi ya shawarci ‘yan siyasa
Khalifa Sanusi II ya ƙara da cewa shugabannin Najeriya suna tunanin kansu, iyalansu, da abokansu kawai.
“Amma mukamin gwamnati amanar jama’a ce,” ya jaddada.
Ya kuma shawarci matasan Najeriya kada su amince da tsarin da ya gurbace wanda suka gada.
Sarkin ya ce ya kamata matasa su haɗa kai domin gina ƙasa irin wacce suke so, ba ƙasar da gazawar shugabanni ta gina ba.
Ya bayyana tsarin yau a matsayin tsarin da aka gina kan rarrabuwar kabilanci, tashin hankalin addini, da neman riba.
“Ƙasa tamu ce. Ba ta gwamnati ko ‘yan siyasa ba,” in ji shi.
“A duk inda muka tsinci kanmu, muna rike da wani ɓangare na Najeriya ne, kuma muna da nauyin bayar da gudummawarmu.”