Jam’iyyar ADC ta yi Allah-wadai da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na umartar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta janye matakin daskarar da asusun Gwamnatin Jihar Osun, tana mai cewa hakan ya nuna cewa hukumar ba ta gudanar da aikinta cikin cikakken ’yanci.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta ce duk da cewa ta yi maraba da janye matakin, umarnin shugaban ƙasar ya tayar da tambayoyi kan matsayin EFCC a matsayin hukuma mai cin gashin kanta.
Jam’iyyar ta kuma ƙalubalanci ikirarin cewa EFCC ta ɗauki matakin ne bisa umarnin kotu, tana mai cewa bayanan da hukumar ta fitar tun farko ba su ambaci wata umarnin kotu ba, sai dai ikon da doka ta ba ta na gudanar da bincike da hana aikata laifuffuka.
ADC ta buƙaci Shugaba Tinubu ya fayyace tushen umarnin kotun da ya ambata, tare da bayyana dalilin da ya sa EFCC ba ta taɓa yin magana a kai ba a bayananta na baya.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa idan har shugaban ƙasa na da ikon ba EFCC umarni kan irin waɗannan batutuwa, to ya kamata ya yi amfani da irin wannan iko wajen umartar Hukumar ICPC da lauyoyinta su daina adawa da neman belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
ADC ta ce hakan zai ƙara tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnati na gudanar da mulki bisa adalci da daidaito ba tare da nuna bambanci ba.