Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta saki tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Atiku ya bayyana cewa idan har shugaban ƙasa na da ikon ba Hukumar EFCC umarni kan yadda za ta gudanar da wasu ayyukanta, to ya kamata a yi amfani da irin wannan iko wajen ba ICPC umarni kan batun El-Rufai.
Ya ƙara da cewa hakan ya sa ake shakkar ikirarin da ake yi cewa Hukumar EFCC na gudanar da ayyukanta cikin cikakken ’yanci ba tare da katsalandan daga gwamnati ba.
Atiku ya ce ya kamata a tabbatar da cewa dukkan hukumomin yaƙi da cin hanci suna gudanar da aikinsu cikin adalci da ’yancin kai ba tare da wani tasiri daga bangaren gwamnati ba.