Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta buɗe shafin neman guraben shiga shirin horas da matasa masu digiri na shekarar 2027 ga ’yan Najeriya da sauran ƙasashen mambobin ƙungiyar.
Shirin, wanda zai gudana na tsawon shekara guda, zai bai wa waɗanda aka zaɓa damar yin aiki a hukumomi da cibiyoyin ECOWAS tare da samun cikakken tallafin kuɗi, horo na musamman da gogewar aiki.
A cewar ECOWAS, masu neman shiga dole ne su kasance ‘yan ƙasar da ke cikin ƙungiyar, shekarunsu ba su wuce 32 ba, sannan su mallaki digiri daga jami’a ko wata cibiyar ilimi da aka amince da ita.
An buɗe karɓar buƙatun ne tun ranar 31 ga Yulin 2026, kuma za a rufe shafin neman guraben a 31 ga Agustan 2026.
Hukumar ta kuma bayyana cewa masu sha’awar shiga shirin za su buɗe asusu a shafin yanar gizon ECOWAS, su cike bayanansu, su loda takardun da ake buƙata kamar shaidar kammala karatu, CV da wasiƙar bayyana dalilin neman gurbin.
ECOWAS ta ce manufar shirin ita ce bunƙasa ƙwarewar matasa, samar musu da gogewar aiki, da kuma gina sabbin ƙwararrun da za su taimaka wajen ci gaban yankin Yammacin Afirka.