Monday, October 19, 2026
HomeTsaroYan bindiga sun saki mutane 176 da aka yi garkuwa da su...

Yan bindiga sun saki mutane 176 da aka yi garkuwa da su – Gwamnatin Kwara

Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da sakin mutanen da aka sace a harin da aka kai ƙauyukan Woro da Nuku da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama a ranar 3 ga Fabrairu, 2026.

Sanarwar ta fito ne ta cikin wani saƙo da gwamnatin ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta tabbatar da cewa mutanen 176 da aka yi garkuwa da su sun samu ’yanci bayan watanni suna hannun masu garkuwa.

Rahotanni sun nuna cewa an sace mutanen ne bayan wasu da ake zargin mayakan masu alaƙa da ƙungiyar Boko Haram sun kutsa cikin ƙauyukan Woro da Nuku a kan babura, inda suka kai harin da ya ɗauki sa’o’i da dama.

Sai dai, zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, gwamnatin ba ta bayyana cikakken bayani kan yadda aka samu nasarar sakin ko ceto mutanen ba. Haka kuma ba a fayyace ko an gudanar da wani samame ko kuma an bi wata hanya ta daban wajen tabbatar da sakin nasu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments