Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBurkina Faso ta saki sojojin Najeriya da jirginsu ya yi saukar gaggawa...

Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya da jirginsu ya yi saukar gaggawa a ƙasar

Burkina Faso ta sako sojojin Najeriya 11 dake tsare a kasar

Wasu bayanai daga Burkina Faso sun ce mahukuntan ƙasar sun saki sojojin Najeriya 11 da ke tsare waɗanda ake zargi da shiga ƙasar ta yankin Sahel ba bisa ƙa’ida ba, bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa a birnin Bobo-Dioulasso sakamakon tangarɗar na’ura.

Rahotanni daga Burkina Faso sun ce, mahukuntan ƙasar da sojoji ke mulka sun ba wa sojojin Najeriya tara da matuƙan jirgin biyu damar fita daga ƙasar, sai dai babu tabbacin ko su amince da sakin jirgin wanda suka ce ya keta tsaron sararin samaniyarsu.

Jirgin wanda ya tashi daga birnin Lagos a Litinin ɗin da ta gabata, na kan hanyarsa ta zuwa Portugal kamar yadda mahukuntan Najeriya ta bakin rundunar sojin saman kasar suka bayyana. Sai dai haɗakar AES da ta ƙunshi ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso waɗanda suka ɓalle daga ECOWAS bayan juyin mulki, sun ce jirgin ƙirar C-130 ya saɓa ƙa’ida bayan keta sararin samaniya da kuma sauka a ƙasar ba tare da izini ba.

Kakakin rundunar Sojin saman Najeriya, Ehimen Ejodame wanda yaƙi cewa komai game da sahihancin bayanan da ke cewa sojin ba su samu izinin keta sararin samaniyar ta Burkina Faso ba, amma ya ce ana ci gaba da bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.

Tun da fari dai haɗakar ta AES ta ce za ta tuhumi mutanen don tabbatar da zargin da ke kansu, ganin yadda lamarin ya zo kwana guda bayan rawar da Najeriya ta taka wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Benin, wanda ya sanya zargin ko jirgin na da alaƙa da aikin.

Sai dai bayanai sun ce haɗakar ta AES da mahukuntan Burkina Faso ba su samu Sojojin Najeriya da hannu a kowanne laifi da suke tuhumarsu ba, wanda ya basu damar komawa gida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments