Sanatan Kano ta Tsakiya kuma Mataimakin Mai Tsawatar da Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa, Rufai Sani Hanga, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NDC.
A cikin wasiƙar murabus mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Agusta, 2026, wadda ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazabar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano, Hanga ya bayyana cewa murabus ɗinsa ya fara aiki nan take.
Sanatan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan nazari da tunani mai zurfi, yana mai cewa ya bar jam’iyyar ne domin mayar da hankali kan wasu al’amuran rayuwarsa da kuma ci gaban aikinsa.
Hanga ya gode wa shugabannin jam’iyyar daga matakin mazaɓa zuwa na jiha da kuma daukacin mambobin NDC bisa irin goyon baya, haɗin kai da damar da suka ba shi a lokacin da yake cikinta.
Haka kuma, ya buƙaci a cire sunansa daga kundin rajistar mambobin jam’iyyar a matakin mazaɓa, tare da tabbatar da cewa ya mayar da katin shaidarsa na zama ɗan jam’iyyar NDC.
Sai dai, Sanata Hanga bai bayyana ko yana da shirin shiga wata jam’iyyar siyasa ba bayan ficewarsa daga NDC.