Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiRibadu: Horon masu tsaron dazuka na kaduna shi ne mafi inganci a...

Ribadu: Horon masu tsaron dazuka na kaduna shi ne mafi inganci a Najeriya

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa shirin horas da masu tsaron dazuka masu ɗauke da makamai a Jihar Kaduna shi ne mafi inganci da aka gudanar a Najeriya zuwa yanzu.

Ribadu, wanda Daraktan Tsaron Cikin Gida na Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), Sani Sani, ya wakilta, ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye rukunin farko na masu tsaron dazuka a Jihar Kaduna.

Ya ce bayan tantance shirye-shiryen horaswa da aka gudanar a jihohin ƙasar, an tabbatar da cewa shirin da Kaduna ta aiwatar ya fi sauran inganci. Ya kuma yi alƙawarin cewa ONSA za ta ci gaba da bai wa jihar goyon baya idan ta buƙaci ƙarin horaswa.

A cewarsa, sama da masu tsaron dazuka 1,000 ne suka samu horo kan amfani da makamai, kula da lafiya, dabarun yaƙi, haɗin gwiwa da jami’an tsaro, mu’amala da al’umma da kuma bin doka yayin gudanar da aikinsu.

Ribadu ya ƙara da cewa ana sa ran waɗanda aka horas za su kasance a sahun gaba wajen kare al’ummominsu daga masu aikata laifuka da ke fakewa a dazuka, kafin isowar jami’an sauran hukumomin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments