Wani bincike da jaridar Punch ta gudanar ya nuna cewa aƙalla cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko (PHCs) guda 6,516 a faɗin Najeriya ba sa aiki, duk da biliyoyin Naira da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suka ware tsawon shekaru domin farfaɗo da su.
Rahoton ya bayyana cewa jihohin Katsina da Osun ne ke da mafi yawan cibiyoyin lafiya da suka daina aiki, lamarin da ke ci gaba da jefa al’umma cikin ƙalubalen samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Binciken ya kuma nuna cewa matsalar ta fi tsanani a Jihar Borno, inda har yanzu ba a sake gina daruruwan cibiyoyin lafiya da rikicin ‘yan ta’adda ya lalata ba.
A cewar rahoton, baya ga lalacewar gine-gine da kayan aiki, ƙarancin ma’aikatan lafiya, matsalar rashin tsaro, ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa da kuma rashin ingantaccen kulawa da cibiyoyin na daga cikin manyan dalilan da ke hana su komawa bakin aiki.