Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSheikh Gumi: Malaman da suka shiga siyasa sun fi waɗanda ke yi...

Sheikh Gumi: Malaman da suka shiga siyasa sun fi waɗanda ke yi wa yan siyasa addu’a

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana ra’ayinsa kan muhawarar da ake yi game da ko ya dace malamai su shiga siyasa ko kuma su tsaya kan wa’azi da karantarwa.

Sheikh Gumi ya ce a ganinsa, shigar malamai cikin harkokin siyasa ya fi anfani fiye da zama a gefe suna yi wa ‘yan siyasa addu’a kawai.

A cewarsa, idan malamai suka shiga siyasa kai tsaye, za su samu damar bayar da gudummawa wajen tsara manufofi da yanke shawarar da za su amfani al’umma, maimakon takaita rawarsu ga ba da shawarwari da addu’o’i daga waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments