Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnati ta musanta ikirarin Atiku kan ribar Naira tiriliyan 7.98 daga ribar...

Gwamnati ta musanta ikirarin Atiku kan ribar Naira tiriliyan 7.98 daga ribar dayen mai

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da ikirarin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, cewa Najeriya ta samu ribar Naira tiriliyan 7.98 sakamakon hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ƙididdigar Atiku ba ta yi la’akari da muhimman abubuwa da ke tasiri wajen lissafin kuɗaɗen shiga daga man fetur ba.

Sanarwar ta bayyana cewa an yi watsi da batutuwa kamar raguwar yawan ɗanyen man da Najeriya ke hakowa, kuɗaɗen samar da mai, da kuma yarjejeniyoyin sayar da ɗanyen mai da aka ƙulla tun kafin hauhawar farashin.

Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma bayyana cewa duk wani ƙarin kuɗin shiga da aka samu sakamakon canjin farashin ɗanyen mai yana bayyana ne ta hanyar rabon kuɗaɗen Tarayya ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

Haka kuma, ta jaddada cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka haɗa da ƙarfafa hanyoyin tara kuɗaɗen shiga, rage gibin kasafin kuɗi da kuma aiwatar da manufofin da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa a nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments