Fitaccen marubuci kuma wanda ya lashe lambar yabo ta Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa wajen dakatar da kashe-kashen da ake zargin jami’an gwamnati na aikatawa ba tare da bin tanadin doka ba.
Soyinka ya bayyana hakan ne yayin gabatar da lacca ta 28 a birnin Fatakwal, inda ya ce kare rayuwar ɗan Adam da tabbatar da adalci su ne ginshiƙan zaman lafiya da ci gaban kowace al’umma.
Ya ce ya sadaukar da laccar bana ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kashe-kashen da ba su dace ba, yana mai jaddada cewa yin shiru kan irin waɗannan abubuwa na ƙara wa masu aikata laifuka ƙarfin gwiwa.
Marubucin ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya su ci gaba da sa ido kan shari’o’in da suka shafi zargin cin zarafin ɗan Adam domin tabbatar da cewa an yi adalci ba tare da son rai ba.
A nasa jawabin, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka, ya bayyana cewa adalci yana farawa ne tun kafin a shiga kotu, yana mai nuna damuwa cewa dubban mutane na ci gaba da zama a gidajen yari ba tare da an yanke musu hukunci ba.