Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKalaman Rarara kan Pantami cin zarafi ne a idon doka – Abba...

Kalaman Rarara kan Pantami cin zarafi ne a idon doka – Abba Hikima Fagge

Lauya mai fafutukar kare haƙƙin al’umma, Abba Hikima Fagge, ya bayyana cewa a mahangar doka, kalaman da fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya yi kan Sheikh Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na iya kai matsayin cin zarafi.

Fagge ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Fact, inda ya yi nuni da hukuncin Kotun Koli na shekarar 1978, wanda a cewarsa ya fayyace yadda doka ke kallon kalaman da za su iya tauye mutunci ko bata sunan mutum.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan sabuwar waƙar Dauda Kahutu Rarara, wadda ta jawo martani da muhawara a kafafen sada zumunta, musamman saboda yadda wasu ke ganin tana ɗauke da zambo ga ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Sheikh Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments