Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeAmurka ta hana shigo da wasu mutum-mutumin zamani daga China saboda tsaro

Amurka ta hana shigo da wasu mutum-mutumin zamani daga China saboda tsaro

Gwamnatin Amurka ta dakatar da kasuwancin sabbin nau’ikan mutum-mutumin zamani (humanoid robots) da ake ƙerawa a China, tana mai bayyana cewa matakin ya shafi kare tsaron ƙasa da rage dogaro da fasahar ƙasashen waje.

China dai ita ce kan gaba wajen ƙera mafi yawan mutum-mutumin humanoid a duniya, lamarin da ya sa matakin Amurka ke iya yin tasiri ga kasuwannin fasaha da cinikayya tsakanin ƙasashen biyu.

Rahotanni sun nuna cewa sabon matakin na daga cikin ƙoƙarin Amurka na ƙarfafa masana’antun cikin gida da kuma rage amfani da fasahohin da take ganin za su iya zama barazana ga tsaron ƙasa.

Masana sun bayyana cewa wannan mataki na iya ƙara tsananta takaddamar fasaha tsakanin Amurka da China, musamman a fannonin ƙirƙirarriyar basira (AI), na’urori masu sarrafa kansu da kuma fasahohin zamani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments